Gwamnatin Tarayya za ta biya Gwamnatin Borno Naira biliyan 9.43 da ta kashe wajen gina gadar sama ta farko da kuma gyaran titunanta da ke sassan jihar.
Kudaden sun hada da Naira biliyan biyar na gyaran hanyoyi da kwalbantoci da kuma biliyan 4.9 da Gwamna Babagana Zulum ya kashe wajen gina gadar saman mai tsawon kilomita biyar a Maiduguri, babban birnin jihar.
- NAJERIYA A YAU: Dalilin da ’yan Majalisa ke son CBN ya sassauta dokar cire kudi
- ‘Amaryata ta haihu wata 3 da aurenmu’
Minista a Ma’aikatar Ayyuka, Umar El-Yakub, ya bayyana cewa, “Sai Kwamitin Tantance Hanyoyi (RAC) ya kammala aikinsa a duk jihohi, sannan a mika rahoton ga Majalisar Dokoki ta Kasa ta amince a biya kudaden.”
Da yake sanar da haka a Maiduguri ranar Laraba, ministan ya kara da cewa, “Gwamnatin Tarayya tana mayar wa gwamnatocin jihohi kudadensu da suka kashe wajen gyaran hanyoyinta.”
A cewarsa, ya ziyarci Jihar Borno ne domin ganin kwamitocin da ma’aikatarsa ta kafa kan aikin tantancewar sun kammala aikinsu domin gabatar da rahoton ga Majalisa ta amince a biya jihohin kudaden.
Da yake tantance gadar saman da ke hanyar Maiduguri zuwa Dikwa, ministan ayyukan ya ce, “Kamfanin da ka ba wa kwangilar bai yi ha’inci ba,” kuma kanana da manyan motocin daukar kaya za su shafe shekarsa 25 suna bi ba tare wata matsala ba.
A cewarsa, kyan tsari da ingancin titin Customs zuwa City Gate mai tsawon kilomita 10 ya kai yadda zai yi gogayya da sauran tituna a kasashen duniya.
A cewarsa, abin da ke kawo wa Gwamnatin Jihar Borno cikas wajen kammala aikin gyaran titin Damboa zuwa Chibok shi ne matsalar tsaro ga ma’aikata da kayan aiki.