Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya jure cin kashin da mutanen da dama a kasar nan ke yi masa.
Yayin wata hira da gidan talabijin na TVC, Masari ya shugaba Buhari ya jima yana hakuri da sukar da ake masa sabanin yadda wasu shugabannin suka gaza jure irin wannan cin kashi da ake musu.
- An tara N315m domin gina masallacin Juma’a a Fataskum
- An harbe mutum 8 ’yan gida daya a masallaci a Afghanistan
Kazalika, Masari ya ce Shugaba Buhari bai gaza ba wajen sauke nauyin alkawuran da ya daukar wa al’ummar Najeriya yayin yakin neman zabe, inda ya bayyana APC a matsayin jam’iyyar da ya kamata ’yan Najeriya su dogara da ita.
“Kada ku manta cewa an yi shugaban kasar da ba ya jure irin wannan cin kashi a kasar nan, amma Buhari ya kau da kansa.
“Sannan duk masu cewa farin jinin jam’iyyar ya ragu to su jira a zo lokacin zabe, kuma yadda jama’a ke kara tururuwar shiga jam’iyyar ya nuna cewa zargin da ake yi mata ba gaskiya bane.
“Ina ganin har yanzu APC ce jam’iyya mafi karfi a kasar nan wacce za a iya dogara da ita a halin yanzu,” in ji Masari.