✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya zubar da hawaye da ya ji an sace Naira tiriliyan uku

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zubar da hawaye lokacin da aka shaida masa yadda wasu suka sace Dala biliyan 16 (kimanin Naira tiriliyan 3 da…

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zubar da hawaye lokacin da aka shaida masa yadda wasu suka sace Dala biliyan 16 (kimanin Naira tiriliyan 3 da biliyan 136 a farashin gwamnati ko Naira tiriliyan 5 da biliyan 40 a kasuwar bayan fage) na kudin sayar da man fetur da iskar gas na kasar nan.
Shugaba Buhari wanda yake kokarin ganin bayan mugun cin hanci da rashawa da ya yi kusan durkusar da kasar nan, ya kasa rike hawayensa ne lokacin da aka shaida masa cewa an sace wannan makudan kudi ne ta hanyar dauko man fetur da a yanzu ake bincike a kai.   
Wata majiya ta ce Hukumar EFCC ta gayyaci daya daga cikin wadanda ake zargi da hannu a almundahanar har sau biyu domin yi masa tambayoyi a baya, kafin a ba da belinsa bisa sanayya, lamarin da aka ce ya fusata Shugaban kasar kamar yadda wata majiya Fadar Shugaban kasa ta shaida wa wata jarida ba Aminiya ba.
Bayanai su ce gwamnatin Amurka tana taimakawa wajen samara da bayanan sirri kan yadda za a gano wasu daga cikin kudaden da aka sace daga Najeriya a asirce. Kuma ana jin kasashen Afirka ta Kudu da Jamhuriyyar Benin suna daga cikin kasashen da ake boye kudaden da aka sace daga Najeriya.
Majiyoyin Fadar Shugaban kasa sun ce kudin da aka sacen an karkatar da su ne daga sayar da man fetur da aka yi da sunan Gwamnatin Tarayya inda suka fada aljifan wadancan mutane.
Wata majiya ta ce: “Ya kamata a ce kuna wurin kuka ga yadda Shugaban kasa ya kadu. Sai dai ya zubar da hawaye lokacin da ya ji mummunar satar da ake tafkawa a kasar nan. Jikinsa ya mutu saboda bayanan sun zo ne a lokacin da kudin shigar kasar nan suka yi matukar raguwa, lokacin da kudin ajiyar wajen kasar nan ba zai iya yi mata komai ba, amma a ce an iske wannan dimbin kudi sun fada aljifan wasu daidaikun mutane.”
Majiyar ta ce sai dai Shugaban kasa ya bayar da umarnin cewa duk kwabon da aka sace a tabbatar an kwato su. Wannan “…ya nuna wasu mutane suna ci gaba da zama wata gwamnati tab daban inda suke yin awon gaba da dukiyar kasa,’ majiyar ta ruwaito Buhari yana fadi.