✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya yi wa ’yan kwallon kwando na mata ruwan Naira

  A shekaranjiya Laraba ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karrama ’yan kwallon kwando na mata na Najeriya da aka fi sani da D’Tigress a…

 

A shekaranjiya Laraba ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karrama ’yan kwallon kwando na mata na Najeriya da aka fi sani da D’Tigress a fadar gwamnati da ke Abuja inda ya yi musu ruwan Naira.

A ranar Lahadin da ta wuce ne dai ’yan kwallon kwando na mata suka daukaka martabar Najeriya bayan sun samu nasarar lashe Gasar kwallon kwando na mata ta Afirka a karon farko bayan sun doke takwarorinsu na kasar Senegal a wasan karshe da ci 65-48 a wasan karshe.  Gasar ta gudana ne a kasar Mali.

Wannan nasara da ’yan kwallon mata suka samu ta sa yanzu su ne za su wakilci Nahiyar Afirka a gasar cin kofin kwallon kwando na mata na duniya da za a yi a shekara mai zuwa a kasar Sifen idan Allah Ya kai mu.

A lokacin da yake tarbarsu a fadar gwamnati da ke Abuja, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi murna game da wannan nasara da ’yan kwallon kwandon suka samu.  Ya ce babu shakka sun daukaka martabar Najeriya a idon Afirka da ma duniya baki daya a game da wannan nasara da suka samu na lashe kofin kwallon kwando na Afirka a karon farko.

Tawagar ’yan kwallon dai ta mika wa shugaban kasar kofin da suka lashe ne a karkashin jagorancin Ministan Matasa da Wasanni Barista Solomon Dalung a fadar gwamnati da ke Abuja. daukacin ’yan kwallon da jami’ansu ne suka samu halartar bikin mika wa shugaban kasar kofin a shekaranjiya Laraba.

Shugaba Buhari nan take ya bayar da umarnin a ba kowace daga cikin ’yan kwallon kwandon da suka samu nasarar lashe kofin Naira Miliyan 1 a matsayin kyauta yayin da jami’ansu za su samu kyautar Naira dubu 500 don nuna farin cikinsa game da wannan kwazo da suka nuna.

“Na bayar da umarnin a ba kowace daga cikinku da kuma masu horar da ku Naira miliyan 1 a matsayin tukwuici kuma lallai kasar nan tana murna da kuma yin alfahari da ku”, inji Shugaba Buhari a lokacin da yake yi musu jawabi.

A nasa jawabin, Ministan Matasa da Wasanni Barista Solomon Dalung ya nuna godiyarsa a madadin ’yan kwallon game da karamcin da ya yi musu na ba su kyautar Naira Miliyan daya kowaccensu.

Wasu daga cikin ’yan kwallon da aka zanta da su sun nuna farin cikinsu game da karramawar da shugaba Buhari ya yi musu inda suka nuna yin haka zai ci gaba da karfafa musu gwiwa musamman a yunkurinsu na tunkarar Gasar cin kofin kwallon kwando na mata na duniya da zai gudana a Sifen a shekara mai zuwa.

Da yawa daga cikin mutanen da aka zanta da su sun nuna farin cikinsu game da kyautar da shugaban ya yi wa ’yan kwallon kwandon, inda suka ce hakan zai karfafa wa na baya gwiwa a duk lokacin da za su wakilci kasar nan a bangaren wasanni.