✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya yi wa Buba Marwa ta’aziyya

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya mika sakon ta’aziyyarsa ga tsohon Gwamnan Jihar Legas a lokacin mulkin soja, Birigediya Mohammed Buba Marwa bisa rasuwar dan uwansa.…

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya mika sakon ta’aziyyarsa ga tsohon Gwamnan Jihar Legas a lokacin mulkin soja, Birigediya Mohammed Buba Marwa bisa rasuwar dan uwansa.

Alhaji Idris Marwa mai shekara 57 a duniya ya rasu ne bayan gajeriyar rahsin lafiya.

Buhari ya aike da sakon ta’aziyyar ne a ranar Talata ta hannun Hadiminsa kan Kafafen Watsa Labarai, Femi Adesina.

Shugaban Kasar ya yi addu’ar Allah Ya jikan mamacin, Ya kuma yi masa rahama.

Ya kara jan hankalin iyalansa da su jure babban rashi wanda ya ce ba su kadai rashin ya shafa ba, rashi ne ga Najeriya baki daya.