Shugaba Buhari ya yi Allah wadai da kisan babban limamin cocin nan, Rabaran John Chietnum, bayan kwana hudu da sace shi a Jihar Kaduna.
Cikin wata sanarwa da shugaban ya fitar a ranar Laraba ta hannun kakakinsa, Garba Shehu, Buhari ya ce lamarin da ban tsoro da kuma rashin ta-ido.
- Iskar gas: Rasha ta jefa kasashen Turai a tsaka mai wuya
- Abin da ’yan Najeriya ke cewa kan sabon karin kudin fetur
Buhari ya ce “Ina cikin tsananin damuwa bisa kisan wannan bawan Allah da wasu bata-gari da suka sha alwashin haddasa fitina a kasar nan suka yi.
“Wannan harin kan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba da ’yan bindiga ke yi na matukar damun gwamnatinmu, saboda saita lamaran tsaro na daga cikin abubuwan da muka ba wa fifiko a yakin neman zaben da ya samar da gwamnatinmu.
“Ina so na tabbatar wa ’yan Najeriya cewa tsayuwata tsayin daka kan kawo karshen lamarin bai sauya ba, domin ina zama da shugabannin tsaro muna tattaunawa kan yadda za mu shawo kan matsalolin da muke da su.
“Ba zan bar su su huta ba har sai an samo mafita mai inganci kan wannan mummunan lamarin, domin samar da tsaro ga mutanen Najeriya shi ne babban abin da muka sanya a gaba.
“Ina kuma tabbatar muku cewa muna da aniyar murkushe makiyan al’umma da duk abin da muka mallaka”, in ji Buharin.
Daga nan sai ya mika ta’aziyarsa ga iyalin mamamcin da kuma kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), reshen jihar Kaduna bisa wannan rashi.