Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya aike da sakon ta’aziyyar rasuwar Sarkin Jama’are, Alhaji Ahmad Muhammadu Wabi III.
Buhari ya aike da sakon ta’aziyyar ne cikin wata sanarwa da hadiminsa kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu ya fitar.
- Dan uwan Jonathan ya kubuta daga hannun masu garkuwa da mutane
- Kalubale da nasarorin da aka samu a gasar AFCON 2021
A cewar sanarwar, “Rasuwar Sarki Ahmad Muhammadu Wabi babban rashi ne wanda ba iya Jihar Bauchi ya shafa ba, har ma da kasa baki daya, duba da irin gudunmawarsa wajen wanzar da zaman lafiya.
“Sarkin mutumin kirki ne wanda ya shafe tsawon rayuwarsa yana mulkar jama’arsa ba tare da nuna bambamci ko wariya ba.
“Shugaba Buhari ya bayyana rasuwar sarkin wanda na daya daga cikin sarakunan da suka dade kan karagar mulki, a matsayin babban rashi.
“Ina yi wa iyalansa, masarautar Jama’are, gwamnatin Bauchi da daukacin al’umma ta’aziyyar rashinsa da aka yi. Allah ya karbi kyawawan ayyukansa sannan ya sada shi da Aljanna,” cewar Shugaba Buhari.
Sarkin na Jama’are ya rasu ne a daren ranar Asabar, sannan aka yi jana’izarsa a ranar Lahadi a fadar masarautar Jama’are da ke Jihar ta Bauchi.