Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nuna alhininsa tare da mika ta’aziyyarsa kan rasuwar tsohon Gwamnan Jihar Kano, Birgediya Dominic Oneya.
Sakon ta’aziyyar Buharin, ta hannun mai magana da yawunsa, Garba Shehu a ranar Juma’a, ta ce Najeriya ba za ta taba mantawa da irin jagoranci Janar Oneya ya yi a matsayin kwamandan soji da kuma harkar wasanni ba.
- Matsalar tsaro: An sake tsawaita hutun makarantun Kaduna
- Bidiyon Dala: Har yanzu Ganduje bai biya ni tarar da kotu ta umarta ba – Jaafar Jaafar
“Najeriya na alhinin rasuwar Janar Oneya, tsohon Gwamnan Soji na Jihohin Binuwai da Kano.
“Ba za mu manta da irin hidimar da ya yi wa al’umma ta hanyar aikin soji da kuma shugabancinsa a Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya, (NFF) ba,” inji Buhari.
Ya kuma mika ta’aziyya ga daukacin al’ummar Najeriya tare da iyalan marigayin.
Kazalika, ya jajanta wa al’ummar Agbarho da ke yankin Ughelli ta Arewa, da gwamnati da kuma al’ummar Jihar Delta kan rashin na Janar Oneya.