✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari ya yi ta’aziyyar rasuwar dan uwan Shehun Borno

Shugaba Buhari ya bayyana mamacin a matsayin abin koyi ga al'umma.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi wa Shehun Borno, Abubakar Ibn Umar El-Kanemi, ta’aziyya game rasuwar dan uwansa, Alhaji Abba Fari Shehu Umar Garbai.

Da yake jajanta wa Shehun Borno, Buhari ya bayyana mamacin a matsayin mutum na gari, jajirtacce wanda ya zama abun koyi ga al’ummarsa.

“Dan uwanka, Alhaji Abba Fari Shehu Umar Garbai, wanda ya kasance mai garin Munguno mutumin kirki ne kuma za a yi rashin shawarwari na gari da ya ke bayarwa.

“Allah Ya jikan sa da rahama, Ya saka masa da mafificiyar Aljanna,” inji Shugaba Buhari, ta sakon ta’aziyyar da hadiminsa kan kafafen watsa labarai, Garba Shehu ya fitar a ranar Talata.

A cewarsa, iyalan El-Kanemi sun shahara wajen neman ilimi da kuma karantar da shi.