✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya yi martani kan sauke Babban Sufetan ’Yan sanda

Doka ta ba Adamu damar ci gaba da kasancewa Babban Sufetan 'yan sanda har zuwa 2024.

Shugaba Muhammadu Buhari da kuma Lauyan Koli na Kasa, Abubakar Malami da ke zaman Ministan Shari’a na Najeriya, sun ce Babban Sufetan ’Yan sanda, Muhammad Adamu na da damar ci gaba da kasancewa a kujerarsa har zuwa shekarar 2023 ko 2024.

Hakan na kunshe ne a cikin wata takardar martani kan karar da wani lauya mazaunin Abuja, Maxwell Opara ya shigar a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, wanda ya kalubalanci ci gaba da kasancewar Babban Sufetan ’Yan sanda a kujerarsa bayan ya kai shekarun ajiye aiki.

Su biyun sun ce lauya Opara ya gaza bayar da wata hujja a shari’ance wadda za ta nuna wanda yake kara bai cancanci ci gaba da kasancewa a kujerarsa ba.

Sai dai Mai Shari’a Ahmed Mohammed ya sanya ranar 30 ga watan Maris domin fara sauraron karar inda ya bai wa Majalisar NPC mai kula da ayyukan ’yan sandan damar gabatar da wanda zai tsaya mata a gaban kotu.

Kamar yadda doka ta tanada, a ranar 1 ga watan Fabrairun 2021 ne ya kamata Babban Sufetan ’yan sanda na Najeriya ya yi ritaya bayan shafe tsawon shekara 35 yana aiki.