✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shekara 1 na mulkin Tinubu ya fi na Buhari muni —CUPP

Al’amuran ƙasar ba kawai sun ƙara taɓarɓarewa ba ne, har ma suna ta ƙara ta’azzara kullum.

Gamayyar Jam’iyyun Siyasa (CUPP) sun yi tur da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Kakakin Ƙungiyar, Mark Adebayo, ya shaida wa manema labarai a ranar Talata a Abuja cewa al’ummar kasar na cikin halin kunci a ƙarƙashin mulkin Tinubu.

Adebayo ya ce akasarin ’yan Najeriya sun ɗauka cewamulkin Tinubu zai kawo ingantaccen sauyi fiye da wanda ya gabace shi, a fannin tattalin arziki, tsaro, ilimi, da lafiya da samar da ababen more rayuwa da dai sauransu.

Ya ce, idan aka yi la’akari da shekara guda na gwamnatin APC, Ƙungiyar CUPP cikin sauƙi za ta iya cewa al’amuran ƙasar ba kawai sun ƙara taɓarɓarewa ba ne, har ma suna ta ƙara ta’azzara kullum.

Ya ce: “A karon farko a tarihin ƙasar nan, Najeriya ta yi baƙin ciki da samun shugaban ƙasa wanda mintinsa na farko a kan mulki jama’a  suka fara fama da wahalhalu da ba a taɓa ganin irinsu ba.

“Tun kafin ya bar dandalin Eagle Square da aka rantsar da shi, ’yan Najeriya suka yi ta tsokaci kan abin da za a iya kira zagon ƙasa ta fuskar tattalin arziki da ya kawo wa ’yan ƙasa koma-baya.

“Ya sanya harkokin kasuwanci suka durƙushe, cin abinci na ƙoƙarin gagarar miliyoyi, da ƙaruwar yara marasa zuwa makaranta, rashin tsaro da yawa da taɓarɓarewar rayuwa, saboda an ƙara farashin man fetur da kusan kashi 600 cikin 100 da kuma hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar ya ninka sau uku.