✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya yi Allah wadai da kisan dalibar da ta zagi Annabi a Sakkwato

Ya kuma ba da umarnin kanwa tare da hukunta masu hannu a ciki

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya yi Allah-wadai da mutanen da suka dauki doka a hannunsu suka kashe Deborah Samuel, dalibar da ake zargi da zagin Annabi Muhammad (S.A.W) a Jihar Sakkwato.

Buhari ya ce kisan abin takaici ne, inda ya ce bai dace mutane su rika daukar doka a hannunsu ba.

A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook da maraicen Juma’a, Buhari ya ce ya ba da umarnin gudanar da bincike don ganowa tare da hukunta masu hannu a ciki.

Ya ce, “Labarin kisan wannan matashiya da ’yan uwanta dalibai suka yi abin tsoro ne matuka, kuma dole ne a yi bincike na gaskiya domin gano me ya faru.

“Hakika, Musulmai a dukkan fadin duniya na girmama dukkan Annabawa, cikinsu har da Annabi Isa (A.S), amma duk inda aka samu ketare iyaka, kamar yadda ya faru yanzu, shari’a ba ta ba kowa damar daukar doka a hannunsa ba.

“Sannan ya zama wajibi malaman addini su ja kunnen mabiyansu cewa mutane ba su da damar daukar doka a hannunsu, dole a kyale hukuma ta dauki mataki.

“Ina yaba wa saurin daukar matakin da Gwamnatin Jihar Sakkwato ta yi, tare da kiran ’yan kasa da su yi amfani da ’yancinsu na fadin albarkacin baki ta hanyar da ta dace.

“Tuni na ba Ministan Yada Labarai da Al’adu da na Harkokin ’Yan Sanda da kuma na Sadarwa umarnin yin aiki da kamfanonin sadarwa wajen dakile kalaman batanci da na yada kiyayya, musamman a kafafen sada zumunta,” inji Buhari.

Daga karshe Shugaban ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan mamaciyar.

A ranar Alhamis ce dai wasu fusatattun matasa suka kashe tare da kone gawar Deborah bayan an zarge ta da zagin Annabi Muhammad (S.A.W) a wani sakon murya da ta aike a dandalin WhatsApp na ajinsu.

Dalibar dai na karatu ne a Kwalejin Ilimi Shehu Shagari da ke Jihar ta Sakkwato.