✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari ya yi alhinin mutuwar Uwargidan Dogarin Shagari

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi alhinin mutuwar Hajiya Nafisatu Galadima Aminu Usman, uwargidan Laftanar Kanar I.G. Usman, babban dogari ga tsohon Shugaban Kasa, Alhaji Shehu…

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi alhinin mutuwar Hajiya Nafisatu Galadima Aminu Usman, uwargidan Laftanar Kanar I.G. Usman, babban dogari ga tsohon Shugaban Kasa, Alhaji Shehu Shagari.

Shugaban Kasar cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata ta bakin mai magana da yawunsa, Mallam Garba Shehu, ya bayyana marigayiya Hajja Nafisatu a matsayin amintacciyar aminiya wacce ta baiwa iyalansa goyon baya na hakika.

Ya yi addu’ar Allah Ya jikanta Ya kuma albarkaci bayanta.

Kazalika, sanarwar ta ce Aisha Buhari, uwargidan Shugaban Kasar ta yi alhinin mutuwar Hajiya Nafisatu wacce ta kasance aminiya a gare ta.