Lauya mai rajin kare hakkin dan Adam, Femi Falana, ya ce ya kamata Shugaba Buhari ya yi afuwa ga duk wani barawon gwamnatin da sauran masu mayan laifuka da ke daure a gidajen yari.
Femi Falana ya bayyana haka ne a yana mai caccakar Buhari kan afuwar shugaban kasa da aka ya yi wa tsohon Gwamnan Jihar Taraba, Jolly Nyami da takwaransa na Jihar Filato, Joshua Dariye, wadanda da aka daure kan satar dukiyar gwamnati.
- Babu sauran abin da Buhari zai iya tsinana wa Najeriya —Kwankwaso
- Ruwan sama: Yadda daminar 2022 za ta bambata a Najeriya
Da yake martani kan yafe wa ’yan siyasar biyu, Falana ya ce afuwar da aka yi musu su kadai nau’i ne na nuna wariya da ba su fifiko a kan sauran fursunoni, alhali su ma din an kama su da laifin satar dukiyar kasa.
“Abin da zan ce shi ne ya kamata a saki duk barayi da masu manyan laifi da ke daure a gidajen yari
“Kundin tsarin mulki ya tanadi kada a fifita tsakanin ’yan kasa da kuma ’yancinsu, sannan daka a yi la’akari da matsayi, jinsi ko wani abu ba.
“Don haka ba daidai ba ne a tsame wasu mutum biyu daga cikin fursunoni a bar sauran ba. Hakan ya saba doka,” inji shi.
Ya kara da cewa zai bukaci lauyoyin da wadanda suke karewa ke tsare a gidajen yari su garzaya zuwa kotu su kalubalanci bambancin da aka nuna wadanda suke karewa.
Tsoffin gwamnonin biyu suna cikin jerin mutum 159 da Buhari ya sanar da yi musu afuwa a lokacin taron Majalisar Kasa da ya jagoranta a ranar Alhamis.
Da yake tsokaci kan afuwar da aka yi wa ‘yan siyasar, Falana ya ce afuwar da aka yi musu su kadai nau’i ne na nuna wariya da fifiko, alhali an kama su da laifin satar dukiyar kasa.
Ya bayyana cewa tun da kundin tsarin mulki ya tanadi a daidaita tsakanin ’yan kasa, to kamata ya yi afuwar ta shugaban kasa ta shafi duk wani wani wanda aka dauri a gidan yari kan laifin sata.
Da yake bayanin a taron cika shekara daya da rasuwar tsohon kakakin Kungiyar Yarabawa ta Afenifere, Yinka Odumakin, Falana ya ce zai nemi lauyoyin fursunonin da tsare su je zuwa kotu su kalubalanci bambancin da aka nuna wadanda suke karewa.