✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya yaba wa kungiyar Super Eagles

Shugaba Muhammadu Buhari ya yaba wa kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles kan nasarar da suka samu kan takwararta ta kasar Zambiya. Buhari ya bayyana…

Shugaba Muhammadu Buhari ya yaba wa kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles kan nasarar da suka samu kan takwararta ta kasar Zambiya.
Buhari ya bayyana nasarar da kungiyar kwallon kafar Najeriyar ta samu da wani abu mai dadi kuma tamkar kyauta ce ta musamman ta bikin cikar kasar shekaru 57 da samun ’yancin kai da suka baiwa al’ummar kasar.
Kungiyar Super Eagles ta lallasa takwararta ta kasar Zimbiya da ci daya da nema a wasan da aka yi a filin wasa na kasa da kasa na Godswill Akpabio da ke garin Uyo a jihar Akwai Ibom a ranar Asabar din da ta gabata.
Wata sanarwa da Mai Baiwa Shugaban Kasar Shawara Na Musamman Kan Harkokin Yada Labarai da Wayar da Kan Jam’a, Mista Femi Adesina ta nuna cewa Shugaban Kasar ya yaba wa kungiyar Super Eagles saboda kokarin da suka yi na sanya kasar ta zama ta farko a nahiyar Afirka da ta samu nasarar shiga jerin kasasen da za su shiga gasar kwallon duniya ta shekarar 2018 da za a yi a kasar Rasha.