Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ranar Asabar ya wuce kasar Afirka ta Kudu domin halartar taron Baje Kolin Kasuwanci na Kasashen Afirka.
Buhari wanda ya bar birnin Paris na Kasar Faransa zai halarci taron irinsa na biyu (IATF, 2021) da za a fara gudanarwa ranar Litinin a Durban.
- ‘Rikicin Boko Haram ya ci malamai 3,798 da makarantu 1,500 a Arewa maso Gabas’
- An kama shi ya yi wa yara ’yan uwan juna fyade
Mai magana da yawun Fadar Shugaban Kasa, Mista Femi Adesina, ya ce za a gudanar da taron ne daga 15 zuwa 21 ga watan Nuwamba, wanda bankin kasuwanci na Afirka, AFREXIM, ke shiryawa da hadin gwiwar Hukumar Kasashen Afirka ta AUC.
“A ranar Asabar Shugaba Buhari zai bar Paris zuwa Durban na Afirka ta Kudu bisa gayyata ta musamman da Shugaba Cyril Ramaphosa ya yi masa don haduwa da sauran shugabannin Afirka a wurin taron Baje-Kolin Afirka 2021,” a cewarsa.
Adesina ya ce tawagar Shugaba Buhari ta kunshi, Ministan Harkokin Waje, Geoffery Onyeama; Ministan Masanaantu, Ciniki da Zuba Jari, Otunba Niyi Adebayo; Darakta Janar na Hukumar Leken Asiri ta Kasa (NIA), Ahmed Rufai Abubakar; da Babban Daraktan Hukumar Bunkasa Kasuwancin Najeriya a Ketare, Segun Awolowo.
Ana iya tuna cewa, Buhari ya bar Najeriya a ranar 31 ga watan Oktoba kwana biyu bayan ya koma gida daga Saudiyya, inda ya halarci taron Sauyin Yanayi a Birtaniya kafin daga baya ya wuce Faransa wurin taron Zaman Lafiya tare da Shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Sanarwar da Fadar Shugaban Kasa ta fitar ta ce ana sa ran Buhari zai koma Najeriya a ranar Talata, 16 ga watan Nuwamba.