Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ayyana ranar 1 ga watan Nuwamban kowace shekara a matsayin ranar matasa ta kasa wato National Youth Day.
Shugaban Kasar ya ware rana ce musamman domin taya matasa murna da yin nazari a kan matsalolin da suka shafe su da kuma gano hanyoyin da za a bi wajen warware su.
Ministan Wasanni da Cigaban Matasa, Sunday Dare, shi ne ya sanar da hakan a shafinsa na Twitter jim kadan bayan kammala zaman Majalisar Zartarwa na Tarayya wanda aka gudanar a ranar Laraba, 2 ga watan Satumba.
- Tsohon Ministan Najeriya daga jihar Kano ya riga mu gidan gaskiya
- Batanci ga Annabi: Falana zai daukaka karar hukuncin kisa
Ga abinda Mista Dare ya wallafa: “Yayin taron majalisa, Shugaba Buhari ya ba da lamunin ware duk ranar 1 ga watan Nuwamba na kowace shekara domin taya matasa murna, da gano hanyoyin warware matsalolin da suke fuskanta.
“Shugaban kasar a koda yaushe yana sadaukar da kai don ganin gwamnatinsa ta jajirce wajen kawo tsare-tsaren da za su amfani matasa. Na gode”.