Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kira ga jami’an tsaron kasar da su tabbata an ceto dukkan daliban da ’yan ta’adda suka sace cikin koshin lafiya.
Wannan kira da Buhari ya yi wa sojoji, ’yan sanda da jami’an hukumar tattara bayanan sirri ta DSS, na zuwa ne bayan sace dalibai da dama da wasu ’yan bindiga suka ka yi a wata Makarantar Sakandire ta Bethel Baptist da ke Kudancin Kaduna.
- Firimiyar Najeriya: Nasarawa United ta tunkudo Pillars daga mataki na biyu
- Na dauki siyasa a matsayin addini — Shekarau
Wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Mallam Garba Shehu ya fitar a ranar Litinin, ta ce Shugaba Buhari ya bayyana damuwarsa kan yawaitar hare-hare da ake kai wa Jihohin Kaduna da Neja kuma galibi suke kare wa a kan dalibai.
“Duk da cewa ana samun ci gaba wajen tura karin jami’an tsaro zuwa yankunan da ke fama da rikici, shugaban ya nemi jami’an tsaro da su gaggauta kubutar da dukkan daliban maza da mata a wadannan yankuna tare da tabbatar da sun koma gida cikin koshin lafiya,” a cewar sanarwar.
Sanarwar ta ce matsalar garkuwa da dalibai wacce ke yawan aukuwa a Arewacin Najeriya, na mayar da hannun agogo baya wajen neman ilimin yara musamman a jihohin da ke baya bayan wajen samun ilimi.
“Shugaban yana kira ga gwamnatocin jihohi da su tabbatar da ka’idar nan ta samar da aminci a makarantu wacce Majalisar Dinkin Duniya ta kawo kuma gwamnatinsa ta karba hannu biyu-biyu.
“Shugaba Buhari ya misalta ayyukan masu garkuwa da mutane a matsayin kasawar masu yinta kuma abin kyama, yana mai Allah wadai da lamarin, wanda yake shafar iyalai da kasa baki daya.”