✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya taya Tinubu murnar zagayowar ranar haihuwa

Shugaba Muhammadu Buhari, ya taya jigon jam’iyyar APC, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu murnar zagayowar ranar haihuwarsa yayin da ya cika shekara 69 a bayan kasa.…

Shugaba Muhammadu Buhari, ya taya jigon jam’iyyar APC, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu murnar zagayowar ranar haihuwarsa yayin da ya cika shekara 69 a bayan kasa.

Buhari cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Mista Femi Adesina ya fitar, ta bayyana cewa Tinubu na ci gaba da samun karbuwa da kuma shiga zukatan al’ummar kasar nan har ma da ketare.

“Farin jinin Tinubu da tasirinsa na ci gaba da karade Najeriya da wajenta”, a cewar Mista Adesina.

Ya ce bikin ranar haihuwar tsohon Gwamnan na Jihar Legas ya zama wata dama da tattauna matsalolin da Najeriya ke fuskanta da kuma shimfida matakan da za su kawo ci gaba a kasar.

Kamar yadda alkaluma na tarihi suka tabbatar, an haifi Tinubu ne a ranar 29 ga watan Maris na shekarar 1952.

A bayan nan ne Aminiya ta ruwaito ana zargin akwai tsamin dangartaka tsakanin Shugaba Buhari da kuma jigon na APC yayin da suka shafe tsawon watanni 14 ba tare da inuwar rumfa daya ta hada su ba.