✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya taya Tinubu murnar cika shekara 72

Buhari ya aike wa Tinubu sakon taya murnar cika shekara 72 a duniya.

Tsohon Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari ya aike wa Shugaba Bola Tinubu, sakon taya murnar cika shekara 72 a duniya.

Buhari ya yaba wa Shugaba Tinubu kan kokarin da yake yi na shawo kan kalubalen da Najeriya ke fuskanta.

Buhari, cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu ya fitar, ya yi wa Tinubu fatan samun nasara da lafiya da tsawon rai da zai yi shugabancin kasar nan.

Buhari, ya yaba wa shugaba Tinubu kan yadda yake “kokarin shawo kan dimbin matsalolin da kasar nan,” ke fuskanta.

“Ni da ‘yan uwana muna addu’ar Allah ya ba ka lafiya da farin cikin ci gaba da yin ayyukan alheri ga kasa. Ina taya ka murnar kara shekara!