Yayin da al’ummar Musulmi ke bikin Maulidin Annabi Muhammad (S.A.W), Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya bi sahu wajen taya su murna.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Alhamis, Buhari ya yi kira ga ’yan kasar musamman Musulmai su yi amfani da lokacin wajen yin wa’azin zaman lafiya da kaunar juna.
- Maulidi: Gwamnati ta ba da hutu ranar Alhamis
- Maulidi na nuna karfin Musulunci ne – Sheik Dahiru Bauchi
Ya ce, “A daidai lokacin da Musulmin duniya ke bikin Maulidi, ina kira ga jama’a su kara jajircewa wajen kaunar juna, soyayya da kuma fahimtar juna.
“Mu yi amfani da lokacin wajen yin hakuri, kwatanta gaskiya, amana da nuna sanin ya kamata a dukkan al’amuranmu”, inji Buhari.
Ranar 12 ga watan Rabi’ul-Auwal a kalandar Musulunci ita ce ranar da Musulmai ke bikin zagoyar haihuwar Ma’aiki (SAW).
Tuni dai Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar a matsayin hutu domin ba Musulmai damar bin sahun takwarorinsu a duniya domin bikin ranar.