Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ranar Lahadin nan ya kama hanyar zuwa birnin Landan na kasar Birtaniya domin duba lafiyarsa.
Hakan na kunshe cikin wani sako da mai bashi shawara kan harkokin kafafen yada labarai na zamani Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na Twitter.
- Haba kungiyar ASUU, a rika sara ana duban bakin gatari
- Sojojin Isra’ila sun kashe Bafalasdine bayan sun zarge shi da caka musu wuka
Fadar Shugaban Kasar ta sanar cewa Buharin zai dawo gida Najeriya nan da makonni biyu.
Tun a ranar 1 ga watan Maris Hadimin Shugaban Kasa kan Yada Labarai, Femi Adesina Buhari zai je ganin likita a Landan bayan ya kammala halartar taro a Kenya, amma sai ya koma Abuja daga Nairobi.
Mutane da dama dai sun bayyana mamakinsu kan yadda Shugaban ya dawo Abuja daga kasar Kenya, a maimakon birnin Landan kamar yadda aka sanar da farko.
Buharin dai ya halarci wani taro ne a birnin Nairobi na kasar Kenya kan cika shekara 50 da kafa Shirin Muhalli na Majalisar Dinkin Duniya (UNEP), inda daga can ne aka tsara zai wuce Landan din don ganin likitocinsa.
A ranar Juma’a da ta gabata ce Fadar Shugaban Kasar ta tabbatar da cewa Buharin ya dawo Abuja.