Shugaba Muhammadu Buhari ya soke gaisuwa da shagulgulan bikin Kirsimeti a bana wanda Shugabannin addinai da na al’umma suka saba yi a babban birnin tarayya.
Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Mallam Garba Shehu ya fitar a ranar Alhamis, ta ce soke shagalin a bana ya yi daidai ta tanadin mahukuntan lafiya da na kwamitin yaki da annobar coronavirus a Najeriya.
- Muryar Sheikh Ahmed Lemu ta kara fito da hasken addinin Islama —Buhari
- Hatsarin mota ya ci mutum uku a Neja
Idan ba a manta ba Shugaban Kasar ya soke shagalin bukukuwan karama da babbar sallah na bana tare da soke gaisuwar sallah da aka saba kai masa duk shekara a ire-iren wadannan lokuta.
Shugaba Buhari ya kuma bukaci ’yan kasar da su yi kiyaye dukkan ka’idodin da aka tanada na nisantar juna, amfani da takunkumin rufe fuska, yawaita wanke hannu da kauracewa wurare masu cunkoson jama’a da kiyaye sauran matakan kariya na dakile yaduwar cutar coronavirus.
Shugaban Kasar ya kuma roki al’ummar Najeriya da su jingine duk wata tafiya wadda ba ta zama tilas ba a wannan lokaci.
Ya kuma taya dukkanin al’umma murnar bikin Kirsimeti da na sabuwar shekara.