A ranar Alhamis din makon jiya ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu a kan dokar mafi karancin albashi na Naira dubu 30.
Mai taimaka wa Shugaban Kasa na musamman a kan Harkokin Majalisun Dokoki (Majalisar Dattawa), Sanata Ita Enang ne ya sanar wa manema labarai haka a Abuja.
Ya ce dokar da aka yi wa kwaskwarima kuma majalisa ta amince da ita wadda ake yi wa lakabi da dokar 2019 (Act 2019), Shugaban Kasar ya rattaba hannu a kanta ce don ganin ma’aikata sun fara cin gajiyar mafi karancin albashi na Naira dubu 30.
Sai dai Sanata Ita Enang ya ce Shugaba Buhari ya hori Kungiyar Kwadago da ma’aikata su ci gaba da nuna kwazo da jajircewa a yayin gudanar da aiki don ganin sun saka wa gwamnati game da wannan karamci da ta yi musu.
“Daga yanzu ya zama tilas ga gwamnatoci da kamfanoni masu zaman kansu su rika biyan ma’aikatansu mafi karancin albashi na Naira dubu 30,” inji shi.
Sai dai dokar ba ta shafi kamfanonin da ke da ma’aikata kasa da 25 ba, kamar yadda dokar ba ta shafi ma’aikatan jiragen ruwa da suke zirga-zirga zuwa kasashen ketare a kowane lokaci ba da kuma kananan masana’antun da ma’aikatansu ba su taka kara sun karya ba.
Ana sa ran ma’aikatan da suka cancanta za su fara karbar mafi karancin albashin ne daga watan gobe (Mayu).