✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari ya sallami Shugaban Hukumar Raya Yankin Neja Delta

Sallamar Mista Akwa na zuwa ne bayan ya shafe kusan shekaru biyu yana rike da wannan mukamin.

Shugaban Kasa Muhammad Buhari ya sallami Shugaban Hukumar Raya Yankin Neja Delta (NDDC), Effiong Akwa.

Darektar Yada Labaru na Ma’aikatar Harkokin Neja Delta, Patricia Deworitshe ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da fitar a wannan Alhamis din.

Sanarwar da aka fitar ta bayyana cewa za a aike da sunayen sabbin mambobin gudanarwa na hukumar zuwa ga Majalisar Wakilai domin amincewa.

Har ila yau, sanarwar ta bayyana cewa shugaba Buhari ya ce korar Effiong Akwa a matsayinsa na Shugaban NDDC zai kasance nan take farawa daga yau 20 ga watan Oktoban 2022.

Sallamar Mista Effiong Okon Akwa na zuwa ne bayan ya shafe kusan shekaru biyu yana rike da wannan mukamin.

An nada Akwa ne a ranar 12 ga Disamba, 2020 bayan da aka tsige Farfesa Kemebradikumo Pondei, mukaddashin Daraktan Shiga Tsakani na NDDC a lokacin.