✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari ya sake nada Farfesa Dambatta Shugaban NCC

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da sake nada Farfesa Umar Garba Danbatta a matsayin Shugaban Hukumar da ke Kula da Harkokin Sadarwa ta Kasa…

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da sake nada Farfesa Umar Garba Danbatta a matsayin Shugaban Hukumar da ke Kula da Harkokin Sadarwa ta Kasa (NCC) a karo na biyu.

Ministan Sadarwa na kasa, Dr Isa Ali Pantami ya bayyana hakan a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Uwa Sulaiman, ta fitar da yammacin Juma’a.

A cewar ministan, sabunta wa’adin shugabancin ya biyo bayan shawarar da ya ba shugaba Buhari na yin hakan ne tun da farko.

Ministan ya shawarci Dambatta da ya rubanya kan kokarin da ya yi a wa’adinsa na farko wajen ganin hukumar ta zarce sa’a ta fannin aiwatar da manufofin gwamnatin ta fuskar sadarwa.

Tun a shekarar 2015 ne dai shugaba Buhari ya nada Dambatta, wanda Farfesa ne a fannin fasahar sadarwa a matsayin shugaban hukumar.