✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari ya sake ganawa da Emefiele 

Wannan dai shi ne karo na uku da Buhari ke ganawa da Emefiele tun bayan cikar wa'adin tsofaffin kudi.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya sake ganawa da Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele a Fadar Gwamnatin Tarayya da ke Abuja.

Ganawar ta ranar Litinin, wanda aka gudanar a sirrince, ita ce karo na uku da aka yi a baya-bayan nan tsakanin bangarorin biyu.

Ana dai zargin ganawar Shugaba Buhari da Gwamnan na CBN ba za ta nasaba da sauya fasalin takardun kudi da aka yi da kuma tababar da biyo bayan sabon tsarin kudin.

Sai dai bayanai sun ce an hangi Emefiele yana barin Fadar Shugaban Kasa, sannan ya ki cewa manema labarai uffan game da abin da ganawarsa da Buharin ta kunsa.

Wannan dai na zuwa ne bayan da Kotun Koli ta dakatar da shirin CBN na aiwatar da wa’adin amfani da tsofaffin kudi.

Idan za a tuna gwamnatocin jihohin Kaduna, Zamfara da Kogi ne suka maka CBN da Gwamnatin Tarayya a Kotun Koli, inda suka bukaci a dakatar da hana mutane amfani da tsofaffin kudin.

Mutane da dama sun bayyana halin kaka-nika-yi da suka shiga biyo bayan canjin kudi da CBN ya yi.

Hakan ya haddasa dogayen layuka a bankunan kasuwanci, inda kwastomomi ke dafifin cirar kudi.

Tun da fari CBN ya ware ranar 31 ga watan Janairu a matsayin ranar daina amfani da tsofaffin takardun Naira, amma daga bisani ya kara wa’adin zuwa ranar 10 ga watan Fabrairu biyo bayan matsin lamba da ya sha daga fadin kasar nan.

%d bloggers like this: