Shugaba Muhammadu Buhari ya sa baki a dambarwar diflomasiyya da ke tsakanin Najeriya da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), wadda ta kai ga kasar ta Gabas ta Tsakiya ta dakatar da bai wa ’yan Najeriya takardar izinin shiga cikinta, wato biza.
A watan Oktobar bara ne hukumomin Daular suka dauki matakin dakatar da bai wa ’yan Najeriya bizar, sai wadanda suke da fasfo na manya wato na diflomasiyya kawai.
- Muna goyon bayan takarar Tinubu —Shugabannin Fulani
- Za mu hukunta duk wanda ya ki karbar tsoffin kudi —Ganduje
Duk da cewa hukumomin kasar ta Larabawa ba su bayyana dalilinsu na daukar matakin ba, wasu na danganta shi ga rashin da’a da bin doka da oda da wasu ’yan Najeriyar da ke zaune ko aiki a can suke yi.
A wata tattaunawa ta waya da Shugaba Buhari ya yi ranar Litinin da takwaransa na Daular, Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan, wanda kuma shi ne Sarkin Abu Dhabi, ya yi maganar neman dage dakatarwar.
Tattaunawar da Shugaba Buharin ya yi da Sheikh Al Nathan na kunshe ne a wata sanarwa da kakakin shugaban na Najeriya Mallam Garba Shehu, ya fitar yau Talata.
Ana iya tuna cewa, Dubai ta soke bai wa ’yan Najeriya bizar ce bayan ’yan makonni da Hadaddiyar Daular Larabawa ta tsaurara matakan bayar da biza ga sabbin bakin da ke marmarin shiga cikin kasar.
Sanarwar da suka fitar tun a bara ta ce, hukumomin kasar sun soke daukacin bukatun neman takardun biza daga ’yan Najeriya da wasu kasashen Afirka na bakaken fata.
Ko a wancan lokaci, mahukuntan na UAE sun ce, ba za su mayar wa ‘yan Najeriya kudaden da suka kashe ba wajen neman takardun bizar da suka soke, yayin da kawo yanzu suka ki bayar da dalilinsu na daukar matakin.