✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari ya roki kamfanoni su dauki matasan Najeriya aiki

Matasan Najeriya masu ilimi da kwarewa a sana'a za su amfani kamfanoni

Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci kamfanoni masu zaman kansu a fadin Najeriya da suka karkatar da sha’awarsu zuwa ga daukan matasa ’yan kasar aiki.

Buhari ya yi wannan kira ne yayin kaddamar da shirin fadada ayyuka na musamman (ESWP) wanda aka gudanar a Abakaliki, babban birnin Jihar Ebonyi ranar Litinin.

Ya ce kaddamar da shirin a fadin kasar na daya daga cikin manufofin gwamnatinsa na tayar da komadar da kasar ta samu bayan gushewar annobar coronavirus da kuma tarzomar zanga-zangar EndSARS.

Ministan Kimiyya da Fasaha, Ogbonnaya Onu wanda ya wakilci Shugaba Buhari a taron ya ce annobar coronavirus wacce ta yi wa ilaharin kasashen duniya ba-zata tun a farkon shekarar 2020, ta haifar da mummunan durkuso na tattalin arziki wanda idan ba a farga ba rashin aikin yi zai ta’azzara a kasar nan.

“Dangane da wannan batu, ina amfani da wannan damar na kirayi dukkanin ma’aikatu masu zaman kansu a kan su ci moriyar matasan Najeriya musamman wadanda suka yi karatu da samun kwarewa a fagen sana’o’i iri-iri don ganin shirin nan da muka kaddamar ya tabbata.”

Shugaba Buhari wanda ya bayyana kwarin gwiwa a kan makomar tattalin arzikin Najeriya, ya ce shirin zai bai wa wasu daga cikin matasan damar samun abin dogaro da kai.

A nasa jawaban, Shugaban Shirin reshen Jihar Ebonyi, Edward Nkewegu, ya ce Gwamnatin Tarayya za ta kashe akalla Naira miliyan 780 wajen fadada shirin cikin watanni uku a Jihar kadai.

“Daga watan Janairu zuwa Maris na bana za a dauki mutum 1,000 a kowace karamar hukumar jihar da za su yi wa Gwamnatin Tarayya aiki.

“Za a rika biyan su N20,000 duk wata na tsawon watanni ukun, wanda a yanzu haka Jihar Ebonyi ta dauki jimillar mutum 13, 000 daga dukkanin kananan hukumominta 13,” in ji shi.

Aminiya ta samu cewa galibin wadanda aka dauki aikin mata ne kuma an damka musu kayan aikin da za su fara a wannan wata.