✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya roki Ganduje filin gina tashar wutar lantarki a Bichi

Ayyukan za su ci N11.3bn kuma za su rika ba wa yankin Kano ta Arewa wutar lantarki.

Gwamnatin Tarayya ta roki Gwamnatin Jihar Kano ta ba ta fili domin gina tashoshin wutar lantarki biyu, masu karfin 132/33kv, a Karamar Hukumar Bichi da kuma garin Kanye a jihar.

Ministan Wutar Lantarki, Injiniya Abubakar Aliyu ne ya mika kokon baran ga Gwamna Abdullahi Ganduje, domin gina kananan tashsohin masu taransfoma biyu kowannensu mai karfin 60MVA a Bichi da kuma garin Kanye.

Wasikar da ministan ya aike wa Gwamna Ganduje ta ce tuni Kamfanin Samar da Wutar Lantarki na Najeriya (TCN) ya isa garin Bichi Kanye domin fara aikin gina tashoshin da za su ci Naira biliyan 11.3 —kowannensu Naira biliyan 5.6 — amma rashin fili ya hana a fara aikin.

Idan aka kammala aikin, tashoshin biyu za su rika samar da wutar lantarkin ne ga yankin Arewacin Jihar Kano.

“Saboda haka Ya Mai Girma Gwamna, za mu yi farin ciki idan ka amince ka ba wa TCN izini da filayen da za a yi wadannan ayyukan a Karamar Hukumar Bichi da garin Kanye,” inji wasikar ministan.

A watan Maris ne dai tsohon Ministan Wutar Lantarki, Injiniya Sale Mamman, ya sanar cewa Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta amince a gina kananan tashoshin wutar lantarkin Bichi da Kanye a Jihar Kano da Zaki Biam a Jihar Binuwai da sauransu.

An bayar da ayyukan wutar lantarkin na Kano ne bisa bukatar Dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Kano ta Arewa, Sanata Barau Jibrin.

– Mun ba da fili —Gwamnatin Kano

Aminiya ta nemi jin ta bakin Gwamna Ganduje game da lamarin, inda ya bayyana mata cewa gwamnatinsa ta kosa ta ga an fara aikin kuma za ta ba da filaye da duk abin da ake bukata daga gare domin a gina sabbin tashoshin.

Sakataren Yada Labaran Gwamnatin Jihar Kano, Abba Anwar, ya ce “An riga an bayar da filayen da za a gina tashoshin, to sai dai ana dab da kammala rubuce-rubuce domin fara aikin, sai gwamnatin jihar ta lura cewa filayen ba su dace sosai da ayyukan ba.

“Yanzu shi ne ta sake bayar da wasu filayen kuma tuni aka riga aka fara duk cike-ciken takardun da ya kamata.

“Muna maraba da wadannan ayyuka domin za su taimaka wajen bunkasa hakokin tattalin arziki a Jihar Kano,” inji hadimin gwamnan.

Abba Anwar ya ce babu mamaki rashin cikakkiyar tuntuba tsakanin bangarorin ne ya sa har ministan ya rubuto takardar neman filayen gina tashoshin.

Daga Sagir Kano Saleh, Simon Echewofun Sunday (Abuja) da Clement Oloyede (Kano)