Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a kan Kudurin Gyaran Dokar Zabe na 2021 da aka dade ana takaddama a kansa.
Buhari ya sanya hannu a kan kudurin ne da misalin karfe 12:25 na ranar Juma’a.
Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan da Shugaban Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila da wasu ‘yan majalisa ne suka shaida sa-hannun.
- UEFA ta dauke wasan karshe na ‘Champions League’ daga Rasha
- NAJERIYA A YAU: Yadda Rikicin Rasha da Ukraine Ya Dugunzuma ‘Yan Najeriya
Shugaban Majalisar Dattawan ya ce dokar da aka sanyawa hannu ta zo da gagarumin ci gaba domin za ta samar da gaskiya ga tsarin zabe.
Sai dai shugaba Buhari ya bukaci Majalisar Dokokin Najeriya ta sake yin aiki don haramta wa masu rike da mukaman siyasa shiga takara, har sai sun cika ka’idojin kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya.
Cikakken bayani ma tafe…