Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da Mai Shari’a Olukayode Ariwoola a matsayin Alkalin Alkalan Najeriya.
An rantsar da Mai Shari’a Ariwoola a wannan Larabar gabanin Buhari ya jagoranci Taron Majalisar Zartarwa a Fadar Gwamnatin Najeriya da ke Abuja.
- Ranar Yara Mata ta Duniya: Yadda jinin al’ada ke hana ni zuwa makaranta
- Shin gwamnati ta saki mayakan Boko Haram kafin ceto fasinjoji jirgin kasa?
Aminiya ta ruwaito cewa, nadin Ariwoola ya biyo bayan ajiye aikin da tsohon Alkalin Alkalai, Ibrahim Tanko Muhammad ya yi a watan Yuni, sakamakon rashin lafiya da ya yi ikirarin yana fama da ita.
A watan Yuni ne dai Buhari ya rantsar da Ariwoola a matsayin Alkalin Alkalan Najeriya na riko, inda ya ci gaba da zaman a wannan mataki har zuwa lokacin da Majalisar Tarayya ta tantance shi a matsayin tabattacen alkalin Alkalan.
Haihuwa da Karatunsa
An haife shi ne a watan Agustan shekarar 1954 a Jihar Oyo.
Babban Jojin ya fara karatunsa ne a Karamar Hukumar Iseyin ta jihar Oyo daga 1959 zuwa 1967.
Ariwoola ya kammala digirinsa a fannin shari’a a Jami’ar Ife wacce ta zama Jami’ar Obafemi Awolowo a Ile Ife da ke Jihar Osun a 1980.
Mai shari’a Ariwoola ya yi karin karatuttuka da kuma kwasa-kwasai a kasashe daban-daban bayan Najeriya da suka hada da Birtaniya da Faransa da Amurka da Birtraniya da UAE.
Aiki da daukaka
Ariwoola ya yi alkalanci a Kotun Daukaka Kara ta Najeriya, kafin ya samu daukaka zuwa Kotun Kolin kasar, inda ya shafe kusan shakara 11 a matsayin daya daga cikin manyan Alkalan Kotun Kolin, bayan shigarsa cikinta a watan Nuwamban 2011.
Kafin ya zama alkalin Kotun Koli dai yana Kotun Daukaka Kara ne a matsayin daya daga cikin alkalanta, sakamakon karin girma da ya samu daga Babbar Kotun Jihar Oyo.
Sannan ya rike matsayin alkali a Kotunan Daukaka Kara na Kaduna da Enugu da kuma Legas.
A yanzu bayan rantsar da shi, ya zama baban jojin Najeriya na 18, kuma ga alama shi ne zai ja ragamar yanke hukuncin shari’ar Zaben Shugaban Kasa na 2023 idan har an samu korafi bayan zaben.
Gwagwarmaya
Mai shari’a Ariwoola na daya daga cin alkalai bakwai na Kotun Koli da suka yanke hukunci kan karar zaben Shugaban Kasa na 2019 da suka tabbatar da Shugaba Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar a karo na biyu.