Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya nada Ahmed Halilu, yaya ga matarsa, Aisha Buhari, a matsayin Shugaban Kamfanin Buga Kudi da Takardun Sirri na Najeriya (NSPMC).
Halilu, ya jagoranci kamfanin a matsayin na riko, bayan murabus din tsohon jagoran kamfanin, Abbas Masanawa, a ranar 16 ga watan Mayun 2022.
- Za a iya daure masu karya dokar hana acaba shekara 3 – Gwamnatin Legas
- Yadda ambaliya ta rusa gidan mutumin da ke rubutu da kafa
Rahotanni sun nuna cewa, Shugaban Kasar ya amince da nadin ne bayan shawarar Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) Godwin Emefiele, wanda ke rike da mukamin shugaban Daraktocin kamfanin.
Halilu, ya shafe sama da shekara 23 yana aiki a harkar banki inda ya yi aiki da bankin AIB da na Zenith.
Ya yi digirinsa na farko a fannin Noma da na biyu a fannin Gudanarwar Kasuwanci da kuma wani a bangaren Diflomasiyya da Harkokin Kasa da Kasa (MIAD) duka a Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zariya.