Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya nada Manjo-Janar Farouk Yahaya a matsayin sabon Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya.
Sanarwar nadin ta fito ne daga Mukkadashin Daraktan Yada Labarai na Hedikwatar Tsaro ta Najeriya, Birigediya Onyema Nwachukwu, a ranar Alhamis.
“Kafin nada shi Babban Hafsan Sojin Kasa, Janar Farouk Yahaya shi ne Kwamandan Rundunar Operation Hadin Kai, mai yaki da ayyukan ta’addanci a yankin Arewa-maso-Gabas.
“Ya kuma taba zama Babban Kwamanda (COG) na Rundunar Soji ta 1 da ke Kaduna,” inji sanarwar Hedikwatar Tsaron.
Gabanin haka, ya yi Mataimakin Sakatare da kuma Sakaren Ayyukan Soji a Hedikwatar Rundunar Sojin Kasa.
An haife Janar Farouk Yahaya a shekarar 1966, yana kuma cikin kananan hafsoshin rukuni na 37 da aka yake a kwalejin soji ta NDA.
Digirinsa na Farko ya yi ne a fannin Tarihi sannan ya yi Digiri na biyu a fannin Diflomasiyya.
A ranar Juma’a, magabacinsa, Laftanar-Janar Attahiru ya rasu a hatsarin jirgin sama tare da wasu jana-janar da wasu sojoji 10 a Kaduna, inda suka kai ziyarar aiki.