Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ayyana Mai Sharia Monica Dongban-Mensem a matsayin Shugabar Kotun Daukaka Kara na riko.
Buhari ya sanar da hakan ne a bukatar amincewa da nadin Mai Shari’a Monica Dongban-Mensem a mukamin da ya aike wa Majalisar Dattawa.
Hadimin Sugaban Kasa a kan Yada Labarai, Malam Garba Shehu ne ya sanar da haka a cikin sanarwar da ya fitar a yammacin nan.
I have sent the nomination of Justice Monica Dongban-Mensem, Acting President, Court of Appeal, to the Senate for confirmation as President, Court of Appeal, in line with the recommendation of the National Judicial Council.
— Muhammadu Buhari (@MBuhari) June 8, 2020
Mai Shari’a Dongban-Mensem alkali ce a Kotun Daukaka Kara, wadda Hukumar Kula da Harkokin Sharia ta Kasa (NJC) ta gabatar wa Shugaban Kasa sunanta domin nada ta a mukamin.