Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin tsohon Gwamnan Jihar Legas na mulkin soja, Birgediya Buba Marwa (mai ritaya) a matsayin sabon Shugaban Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA).
Kakakin Shugaban Kasar, Malam Garba Shehu ne ya tabbatar da hakan a ranar Asabar yayin da yake amsa tambaya kan gaskiyar jita-jitar da ake yadawa kan nadin.
- Tashar Buhari: Da N30 sai a kai ka har gida a Kano
- Museveni ya lashe zaben shugaban kasar Uganda a karo na shida
Garba Shehu ya ce,“Gaskiya ne Shugaban Kasa ya amince da nadin Buba Marwa a matsayin sabon Shugaban Hukumar NDLEA.”
Ya ce nadin nasa ya fara aiki ne nan take.
Kafin nadin nasa, Buba Marwa shi ne shugaban Kwamitin Dake ba Shugaban Kasa Shawara kan Yaki da Miyagun Kwayoyi (PACEDA) tsakanin shekarun 2018 zuwa 2020.
A lokacin dai ya ba da gudunmawa matuka wajen tsara jadawalin yadda za a kawo karshen ta’ammali da miyagun kwayoyi a Najeriya.
Ya yi karatunsa ne a Makarantar Sojoji (NDA) da ke Kaduna, kafin daga bisani ya wuce zuwa Jami’o’in Harvard da ke Birtaniya da ta Pittsburgh a Amurka inda ya yi digirorinsa na biyu a sassa daban-daban.