Shugaba Buhari ya gabatar da bukatar karin kasafain kudi na biliyan N895 ga Majalisar Tarayya domin amincewarta.
Shugaban Kwamitin Sojan Kasa a Majalisar Dattawa, Sanata Ali Ndume ne ya bayyana hakan ranar Juma’a a Abuja bayan ganawar sirri tsakaninsa da Babban Hafsan Sojan Kasa, Manjo-Janar Farouk Yahaya.
- Shekau ya zabi a yi masa azaba a lahira —Shugaban ISWAP
- Matan Birnin Gwari sun amince maza su doke su
Sanata Ndume ya ce: “Shugaban Kasa ya ba mu tabbacin zai sake fasalta hukumomin tsaro; Bukatar karin kasafin kudin tana nan a gabanmu kuma za mu yi gaggawar amincewa da ita.”
Da yake magana bayan tabbatar da shi a mukamin Babban Hafsan Sojin Kasa, Manjo-Janar Farouk Yahaya ya ba da tabbacin cewa dakarun rundunar za su ci gaba da bayar da gudummawarsu ta fuskar dakile matsalolin tsaro a kasar nan.
A ranar Laraba Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta amince da daftarin karin biliyan N895 na kasafin kudin 2021 domin sayo makamai da kuma allurar rigakafin COVID-19.
Ministar Baitul Mali da Tsare-tsare, Zainab Ahmed, ta ce daftarin ya kunshi biliyan N770.6 da za a kara karfafa rundunonin tsaro domin tunkarar kalubalen da ake fuskanta a Najeriya a halin yanzu.
Biliyan N83.56 kuma an tanadar da shi ne domin sayowa da ma jigilar allurar rigakafin COVID-19 daga kamfanin Johnson and Johnson.