Sa’o’i kadan bayan ’yan Majalisar Dattawa sun yi barazanar tsige shi kan matsalar tsaro a Najeriya, Shugaban Kasa Muhamamdu Buhari ya kira taron Majalisar Tsaro ta Kasa a ranar Alhamis.
’Yan majalisar, a zamansu na ranar Laraba, sun bai wa shugaban kasar wa’adin mako shida ya kawo karshen matsalar tsaro da ta yi wa Najeriya dabaibayi, in ba haka ba su tsige shi.
- Lauyan Abduljabbar ya zargi alkali da hadin baki da gwamnatin Kano
- NAJERIYA A YAU: Matsalar Tsaro Za Ta Iya Kawo Wa Zaben 2023 Cikas
Sun yi barazanar tare da ficewa daga zauren Majalisar ne bayan Shugaban Majalisar, Sanata Ahmad Lawan, ya ki bari a tattauna batun, wanda Shugaban Marasa Rinjaye, Sanata Philip Aduda ya dauko.
Amma da yake martani ka barazanar, Ministan Yada Labarai da Raya Al’adu, ya ce Buhari na yin duk abin da ya kamata, ba dare, ba rana, domin kawo karshen matsalar tsaron da a baya-bayan nan ta yi kamari.
“Ina tabbatar muku cewa shugaban kasa na sane da duk abin da ke faruwa, kuma ina kyautata zaton gobe (Alhamis) za a yi wani taron Majalisar Tsaro ta Kasa; wannan (a’amarin tsaro) abu ne da shugaban kasa ba ya wasa da shi.
“Kamar yadda na sha fada kuma, wasu daga cikin matakan da muke dauka ba abubuwa ba ne da za a fito bainar jama’a ana yayatawa.
“Amma abin ya mu, kuma ba za mu yi watsi da nauyin da ya rataya a kanmu ba,” inji ministan.
A cewarsa, Fadar Shugaban Kasa tana yaba wa Sanatocin bisa yadda suka nuna damuwa kan matsalar tsaron, yana mai ba su tabbacin cewa tuni bangaren zartarwa na yin abin da ya kamata domin yi wa tufkar hanci.
A baya-bayan nan mastalar tsaro ta addabi yankin birnin Tarayya Abuja, inda wani hari ya sa aka rufe Makarantar Sakandaren Gwamnatin Tarayya da ke Kwali a ranar Litinin.
A ranar Lahadi da dare kuma ’yan ta’adda sun kashe sojojin rundunar da ke tsaron shugaban kasa a wani harin kwanton bauna.
Sojojin sun gamu da ajalinsu ne a hanyarsu ta dawowa daga Makarantar Koyon Aikin Lauya da ke Bwari, inda suka je gudanar da binciken sharar fage da daukar matakan tsaro bayan ’yan ta’adda sun aike wa hukumar makarantar wasikar barazanar hari.
Daga baya dai an dauke gudanar da bikin yaye sabbin lauyoyi da aka gudanar ranar Laraba daga harabar makarantar zuwa Sakatariyarta da ke yankin Jabi.
Duk wannan na zuwa ne bayan ’yan bindigar da suka sace fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna sun yi barazanar sace Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
Amma a martaninsa kan barazanar, Lai Mohammed, ya bayyana shi matsayin abin dariya.
Sai dai wasu tsofaffin na hannun daman Buharin wadanda a yanzu ba sa ga maciji, Alhaji Buba Galadima da kuma Hajiya Najaatu Muhammad na ganin sabanin hakan.
Najaatu, a hirarta da Sashen Hausa na Rediyon Faransa (RFI) ta ce Buharin bai fi karfin ’yan ta’adda su sace shi ba.
Ta ce tunda har suka iya kai wa ayarin motocinsa hari, duk da cewa ba ya ciki, to ai sun riga sun karya shi.
Daga Sagir Kano Saleh, Muideen Olaniyi da Abdullateef Salau.