Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ki amincewa da kudurin da Majilsa ta aika masa na kafa peace corps.
Shugaban ya aika da takardar kin amincewarsa ne a wata takarda da Shugaban Majalisar Wakilai Yakubu Dogara ya karanta a zauren majalisar a ranar Talata.
Idan za a iya tunawa, majalisar ta amince da kudirin kafa jami’an tsaron ne tun a shekarar 2015 bayan an ta samun rikici tsakanin jami’an na peace corps da wasu jami’an tsaron kasa.