✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari ya karrama dan sandan da ya ki karbar cin hancin dala dubu 200 a Kano

An bukaci hadin kan jama’a domin ganin an dakile ayyukan cin hanci a tsakanin al’ummar Najeriya.

Shugaba Muhammadu Buhari ya karrama hazikin dan sandan nan, SP Daniel Amah da ya ki karbar cin hancin dala dubu 200 yayin wani bincike kan wata ta’adar fashi da makami a Jihar Kano.

Buhari ya jinjina wa SP Amah da ke zaman DPO a wani caji ofis a Karamar Hukumar Nasarawa da ke jihar Kano.

Buhari ya karrama DPOn wajen taron da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta ICPC ta shirya domin tattauna batutuwan da suka shafi cin hancvi da rashawa a tsakanin Ma’aikatan Gwamnati.

SP Amah ya nuna kwarewa da kuma kyamar cin hanci lokacin da ya gudanar da aikin sa na kama wani da ake kira Ali Zaki da wasu jami’an ‘yan sanda dangane da fashin kudin da ya kai naira miliyan 320.

Kafin wannan lokaci, Sufeto Janar na ‘yan sandan kasar, Alkali Baba ya yaba wa DPOn saboda abinda ya kira kwarewarsa da jajircewa da kuma nuna bajinta wajen gudanar da aiki.

Shugaban Hukumar ICPC, Farfesa Bolaji Owasanoye ya bukaci hadin kan jama’a domin ganin an dakile ayyukan cin hanci a tsakanin al’ummar Najeriya.