✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya kai ziyara Daura

Shugaba kasa zai yi mako guda a Jihar Katsina mai fama da ’yan bindiga

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kai ziyara mahaifarsa, Daura, Jihar Katsina inda zai shafe mako guda.

Mai magana da yawun Shugaban Kasa, Garba Shehu ne ya sanar da haka da almurun ranar Juma’a.

“Yanzu haka helikwatan Shugaba Buhari ya sauka a Daura a ziyarar da Shugaban Kasa ya kai ya kai na mako guda.

“Rabonshi da zuwa Daura tun watan Disamban 2019 Buhari, tsawon lokaci bayan bullar annobar COVID-19.

“A tsowon zaman da Shugaban Kasa zai yi a Daura, zai kai ziyarce-ziyarce na kashin kai sannan zai halarci taron Majalisar Zartarwa ta Kasa ta bidiyo ranar Labara, wanda Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo zai jagoranta”, inji Garba Shehu.

Tun hawansa mulki a shekarar 2015, Shugaban Buhari ke yin Babbar Sallah a Daura, amma a 2020 a Abuja ya yi Babbar Sallar Idin Babbar Sallah tare da iyalansa domin kiyaye matakan kariyar cutar COVID-19.

Jihar Katsina na daga cikin jihohi mafiya fama da matsalar tsaro a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.

‘Yan bindiga masu garkwa da mutane, satar shanu da fashi da makami sun addabi yankunan inda suke haddasa asarar rayuka da dukiyo.

Ayyukan ‘yan bindiga a yankin ya kai ga kona kauyuka, yi wa mata fyade, garkuwa da mutane da sauran na’ukan ta’addanci.