Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da kafa kwamitin da zai tabbatar da mika mulki ga wanda zai gaje shi bayan cikar wa’adinsa a watan Mayu.
Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha ne ya bayyana hakan ranar Alhamis a Abuja, a cikin wata sanarwa da Dataktan Yada Labarai a ofishinsa, Willie Bassey, ya fitar.
Buhari dai zai mika mulki ne ranar 29 ga watan Mayu mai zuwa lokacin da zai kammala wa’adinsa na shekara takwas.
A cewar sanarwar, mambobin kwamitin sun hada da Sakataren Gwamnatin Tarayya a matsayin Shugaba da Shugaban Ma’aikata na Tarayya da Babban Sakataren ma’aikatar Shari’a da ta Tsaro da ta Cikin Gida da kuma ta Kudi, Kasafi da Tsare-tsare.
Sauran sun hada da Manyan Sakatarorin ma’aikatun Harkokin Waje da ta Yada Labarai da Al’adu da Babban Birnin Tarayya Abuja da Ayyuka na Musamman da Ofishin Sakataren Gwamnati.
Kazalika, akwai kuma Manyan Sakatarori a ofishin Tattalin Arziki da na Siyasa da na Fadar Shugaban Kasa da Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Kan Harkokin Tsaro da Babban Hafsan Tsaro na Kasa da Sufeto-Janar na ’Yan Sanda da Shugaban Hukumar Leken Asiri ta Najeriya (NIA) da Shugaban Hukumar Tsaron Farin Kaya Babban Magatakarda na Kotun Kolin Najeriya.
“Sakataren Gwamnatin Tarayya ne zai rantsar da kwamitin ranar Talata, 14 ga watan Fabrairun 2023 da misalin karfe 12:00 a dakin taron ofishinsa. Ana bukatar mambobin kwamitin su hallara da kansu,” in ji sanarwar.
Za a mika mulkin ne ga duk wanda ya sami nasara a zaben da za a gudanar ranar 25 ga watan Fabrairu.