A jiya Talata ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya kaddamar da motocin yaki na sojoji da aka kera a Najeriya, wanda ake kira ‘Mine Resistant Ambush-Protected vehicles (MRAPs)’. Masana’antar kera makamai na Najeriya (DICON) ce ta kera motocin.
Wadannan motocin da aka kaddamar zasu taimaka wajen yakar ‘yan ta’adda da ke kawo barazana ga tsaron kasar, musamman yankin Arewa maso Gabas.
Shugaban Najeriya ya radawa motocin yakin suna Ezegwu.
A yayin kaddamar da motocin a Kaduna, Shugaba Buhari ya jinjinawa dakarun Najeriya wajen kwazon tabbatar da zaman lafiya a Najeriya.
