✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya kaddamar da kasuwar zamani a Zariya

Bikin kaddamarwar ya gudana ne a ci gaba da ziyarar aiki na kwanaki biyu da ya kai Jihar Kaduna.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ranar Juma’a ya kaddamar da babbar kasuwar Sabon Garin Zariya wadda aka mayar da ita ta zamani.

Bikin kaddamarwar ya gudana ne a ci gaba da ziyarar aiki na kwanaki biyu da ya kai Jihar Kaduna domin kaddamar da ayyukan da gwamnatin Jihar ta aiwatar.

Shugaba Buhari ya ce irin ayyukan da ya gani da idonsa ya gamsu da tsare-tsaren Gwamna Nasiru El-Rufa’i ke yi a Jihar.

Shugaba Buhari, lokacin da yake kaddamar da kasuwar a Sabon Garin Zariya

A lokacin ziyarar kuma, Shugaban ya kaddamar da wasu daga cikin hanyoyin da aka kammala tare da duba wadanda ake ci gaba da aikinsu.

Tun da farko a jawabinsa, Gwamna Nasiru El- Rufa’i, ya bayyana ziyarar da Shugaban ya kawo Jihar domin kaddamar da ayyukan ci gaba abin alfahari ne ga al’ummarta baki daya.

Gwamnan ya kuma roke shi da ya sake kawo ziyarrar aiki kafin karewar wa’adinsa, don kaddamar da saran ayyukan da ake ci gaba da su.

A nasa jawabin, Mai Martaba Sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli, ya bayyana godiya bisa daukin da ya kai wa asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello sadoda ya sami ingantuwa tare da dawo da martabarsa.

Ya kuma yi amfani da damar inda ya koka bisa yadda harkan tsaro ke barazana ga zamantakewar al’ummar.

Sarkin ya ce a duk rana sai ya sami rahoton harin ’yan ta’adda sun kai hare-hare ga al’ummomi tare da neman kudin fansa.