✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari ya kada kuri’a a Daura

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a kada kuri'arsa a mazabarsa da ke Daura a Jihar Kasina.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a kada kuri’arsa a mazabarsa da ke Daura a Jihar Katsina.

Buhari da iyalansa sun jefa kuri’arsu ne a rumfar zabe ta Sarkin Yara da ke Daura.

Tun a ranar Alhamis shugaban kasa da iyalan nasa suka isa Daura domin zabe, jim kadan bayan kammala yakin neman zabe.

Ko a ranar sai dai shugaban kasar ya halarci taron karshe na yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyarsa ta APC, Bola Tinubu a Jihar Legas.