✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya je wurin fareti sanye da kakin soja

Sojoji 1,000 ke gabatar da faretin da Buhari da Hafsoshin Tsaro ke halarta

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya fito sanye da kakin sojoji a dandalin Eagles Square inda sojoji ke fareti a safiyar Alhamis. 

Buhari ya isa dandalin, inda sojoji 1,000 ke gabatar da fareti inda ya samu rakiyar Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Ibrahim Gambari.

Babban Hafsan Taron Najeriya, Janar Lukcy Irabor da Babban Hafsan Sojin Kasa, Laftanar-Janar Faruk Yahaya da kuma Shugaban ’Yan Sandan Najeriya, Usman Baba na daga cikin mahalarta faretin.

Sauran hafsoshin tsaro da Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan na daga cikin mahalarta faretin sojojin.