Majalisar Tsaro ta Kasa ta yi wata tattaunawa karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari.
An gudanar da taron ne a Fadar Shugaban Kasa kimanin kwana uku kafin zaben shugaban kasa da ’yan Majalisar Dokoki ta Kasa da za a gudanar ranar 25 ga watan da muke ciki.
Mahalarta zaman na ranar Laraba sun hada da Babban Hafsan Tsaro, Janar LEO Irabo, Shugaban ’Yan Sanda, Usman Baba Alkali, da kuma ministoci da mashawartan shugaban kasa kan harkokin tsaro.
Gabanin fara taron, Buhari ya kaddamar da wasu kayayyakin tsaro da Gamayyar Kungiyoyin Yaki da COVID-19 ta bayar tallafi.