✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya jaddada kudurinsa na inganta Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da kokari don samar da mafita ga kalubalen da kasar take fuskanta. A wata sanarwa…

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da kokari don samar da mafita ga kalubalen da kasar take fuskanta.
A wata sanarwa da Mataimaka Masa na Musamman kan Harkokin Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Malam Graba Shehu ya sanya wa hannun a jiya  ya ce shugaban ya yi furucin yayin da yake karbar tawagar membobin kungiyar Manoma da kungiyar ’Yan kasuwa da  kungiyar Matasa da kungiyar Dattawa da kuma ’yan siyasa a garin Daura da ke jihar Katsina.
Shugaba Buhari wanda ya ba ’yan Najeriya tabbacin kara kaimi don bautawa kasarsa ya alakanta samun lafiyar da ya yi ga wani al’amari na Ubangiji.
Buhari ya ce ya dawo kasar ne da burin bin diddigin dokokin da za su inganta rayuwar al’ummar kasar.