Shugaba Muhammadu Buhari ya sauka a Kano domin kaddamar wa wasu manyan ayyuka a safiyar Litinin.
Aminiya ta gano ceewa sabanin yadda aka saba, al’ummar da suka fito domin tarbar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ba su taka kara sun karya ba a yankin Fadar Sarkin Kano Sarkin Kano. Alhaji Aminu Ado Bayero.
Akasarin su yara ne kanana da kuma Almajirai.
Buhari ya kai ziyarar ce washegarin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya kara wa’adin daina karbar tsoffin dakardun Naira.
Hakan kuwa na zuwa ne bayan kwan-gaba-kwan-baya da aka yi ta yi kan ziyarar tsakaninsa da Gwamnatin Jihar Kano.
Karin bayani na tafe.