✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya gargadi Fayose kan alkanta matarsa da badakalar kudi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi watsi da wani kage da Gwamnan Jihar Ekiti Mista Ayo Fayose ya yi a kan matarsa A’isha Buhari, inda…

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi watsi da wani kage da Gwamnan Jihar Ekiti Mista Ayo Fayose ya yi a kan matarsa A’isha Buhari, inda ya danganta ta da wata badakalar cin hanci a Amurka.
Kakakin Shugaban kasa Malam Garba Shehu, ya fadi a wata sanarwa cewa bai kamata a bar Fayose ya dulmiyar da ’yan Najeriya da zantukansa “na karya” ba.
“Muna gargadi da kakkausar murya ga Mista Fayose ya san cewa A’isha Buhari na da damar kare mutuncinta.”
Malam Garba Shehu ya kara da cewa ya kamata Gwamna Fayose ya shiga taitayinsa ya san cewa bambancin siyasa ba lasisi ba ne na cin zarafin jama’a.
A ranar Litinin ne Gwamna Fayose ya shaida wa kafofin watsa labarai cewa, A’isha Buhari na da hannu a badakalar cin hanci da ta hada da wani dan Majalisar Dokokin Amurka, Mista William Jefferson da aka yanke wa hukunci a shekarar 2009.
Ana ganin Fayose ya rudu ne da farfagandar da gidan rediyon Biyafara ke yadawa kan wannan zargi ya yi wannan katobara, alhali A’isha Buharin da ake magana, ba matar Shugaban kasa ba ce.
Fadar Shugaban kasa ta ce, A’isha Buhari ba ta da hannu ko wata alaka da wannan badakala da Fayose ya danganta ta da ita.
Gwamna Ayo Fayose wanda ke sahun gaba a jerin ’yan adawar da ke sukar manufofin gwamnatin Shugaba Buhari da kuma Jam’iyyar APC mai mulki a ranar Litinin ya bara cewa gwamnatin ta rufe masa asusun ajiyar bankinsa, inda ya yi barazanar daukar mataki matukar ba a bude asusun cikin awa 24 a ranar Talatar da ta gabata ba.
Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) wadda ta rufe asusun ta ce tana zargin an yi amfani da asusun ne wajen boye kudin haram, sai dai ba ta bayyana ko nawa ne ba. Amma wata majiyar tsaro ta shaida wa jaridar Premium Times cewa an yi amfani da wani kamfani mai suna Silber Magna Merra Limited da ake alakanta shi da ’ya’yan tsohon Minista a Ma’aikatar Tsaro, Musliu Obanikoro, wato Gbolahan da Babajide Obanikoro, wajen tura Naira biliyan daya da miliyan 300 na kudin tsaro zuwa asusun na Fayose daga ofsihin tsohon Mashawarcin Shugaban kasa kan Tsaro Kanar Sambo Dasuki.
Sai dai kakakin Fayose, Mista Lere Olayinka, ya shaida wa jaridar Premium Times din cewa Gwamnan bai amshi wani kudi daga Obanikoro ba, kuma babu wata harkar kudi da aka gano a asusun na Fayose. “Babu wata Naira biliyan daya da miliyan 300 da aka gano a asusun Gwamnan. Bai amshi wani kudi daga Obanikoro ba, kuma babu wata harkar kudi a asusunsa daga Obanikoro,” ya aike da sako ta shafinsa na Whatsapp ga jaridar.